Mun fara sabuwar shekara da kafar dama - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Van Gaal yana shan matsi kan yadda ya ke jagorantar United

Louis Van Gaal ya ce doke Swansea 2-1 da suka yi a ranar Asabar a gasar Premier, ya kara musu kwarin gwiwa da zai sa su kara azama a 2016.

Kafin United ta kara da Swansea sai da ta yi wasanni takwas ba tare da ta samu nasara ba, kuma rabon da ta yi hakan tun a shekarar 1990.

Kuma nasarar da United ta samu a kan Swansea ya sa ta koma mataki na biyar a teburin Premier da maki 33 daga wasanni 20 da ta buga a gasar.

Kociyan ya ce abin farin ciki ne yadda 'yan wasa suka buga karawar kamar yadda suka shirya duk da matsin da suka fuskanta daga Swansea.

Van Gaal ya ce yana fatan nasarar da suka samu ta dawo da tagomashin Manchester United musamman da aka shiga sabuwar shekara.