Na hukunta Sadio Mane saboda makara - Koeman

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Saido Mane ya koma Southampton da taka leda daga Red Bull Salzburg a shekarar 2014

Kociyan Southampton, Ronald Koeman, ya ce ya hukunta Sadio Mane kan makara zuwa taro da 'yan wasa, shi ya sa bai fara saka shi a wasan da suka yi da Norwich ba.

A ranar Asabar Norwich ta doke Southampton da ci daya ba ko daya a wasan Premier da suka buga gasar mako na 20.

Sai da ya rage saura minti 10 a tashi daga karawar ce Koeman ya saka Sadio Mane.

Koeman ya ce a bara ma sai da dan wasan ya makara zuwa wajen atisaye, kuma yanzu ya kara makara a ganawar da aka shirya yi da 'yan jaridu.

Kociyan ya ce wannan halayyar rashin girmamawa ce ga 'yan wasa da kungiya domin suna biyan makudan kudade domin su kalli 'yan wasa.