Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Alin Tarara da Kurarin Kwarkwada kuma turmi uku suka yi babu kisa a wannan takawar

Wasanni tara aka yi gumurzu a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria da safiyar Lahadi.

A kuma karawar da aka yi wasanni biyu ne aka yi kisa, shi ne wanda Shagon Kugiya daga Kudu da ya buge Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa a turmi na uku.

Sai wanda Shagon Shagon Autan Faya daga Kudu da ya buge Aljani Mai Carbi daga Arewa a turmi na biyu.

Dogon Bunza daga Arewa ya sha zuga a wajen makadin 'yan dambe Autan Mai Turare, kuma Dan Kanawa daga Kudu ya nemi su taka amma ya ki.

Ga wasannin da aka yi babu kisa ciki har da karawa uku da Kurarin Kwarkwada daga Kudu da ya yi dukkansu babu kisa.

  1. Shagon Shagon Alhazai daga Arewa da Shagon Shagon Autan Faya daga Arewa
  2. Shagon Bahagon Fandam daga Kudu da Shagon Sunusi Dan Auta daga Arewa
  3. Dogon Na Manu daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu
  4. Dakakin Dakaka daga Kudu da Fijot daga Arewa
  5. Bahagon Alin Tarara daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu
  6. Kurarin Kwarkwada daga Kudu da Soja daga Arewa
  7. Shagon Autan Faya daga Kudu da Shagon Alhazai Mai Kura daga Arewa