An amince wa Guinea ta karbi bakuncin tamaula

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Agusta ne Caf, ta dakatar da Guinea daga karbar bakuncin wasannin tamaula

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta dage takunkumin da ta dorawa Guinea kan karbar bakuncin wasannin kwallon kafa a kasarta sakamakon cutar Ebola.

Caf din, a wasikar da ta aikewa hukumar kwallon kafar Guinea a ranar Litinin, ta ce daga yanzu kasar za ta iya saukar duk wata tawagar kwallon kafa domin fafatawa da ita a cikin kasarta.

Hukumar kwallon kafar Afirka ta dauki wannan matakin ne bayan da hukumar lafiya ta duniya ta wanke kasar Guinea daga cikin kasashen da ke dauke da cutar Ebola a duniya.

Tun a cikin watan Agustan 2014 ne Caf ta dakatar da Guinea daga karawa da wata tawagar a cikin kasarta.