Chelsea ta warware — Hiddink

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hiddink na kokarin maidoda Chelsea a kan hanya

Kocin riko na Chelsea, Guus Hiddink ya ce kungiyar za ta kammala gasar Premier ta bana a cikin kungiyoyi hudu na farko, bayan da ta doke Crystal Palace da ci uku da nema.

Babu kungiyar da ta samu galaba a kan Chelsea a cikin wasanni hudu da suka wuce, amma a yanzu Tottenham wacce ke matsayin na hudu, ta bai wa Chelsea din tazarar maki 13.

"Abin na da wuya, gasar tana da zafi, kuma kowacce kungiya za ta iya samun nasara," in ji Hiddink.

Ya kara da cewa "Komai na iya faruwa akwai sauran wasanni."

Hiddink ya maye gurbin Jose Mourinho a cikin watan Disamba bayan da kungiyar ta fuskanci rashin tabbas a gasar.