Real Madrid ta kori Rafa Benitez

Wasansu da Valencia ne ya kara jefa Benitez cikin matsala

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Wasansu da Valencia ne ya kara jefa Benitez cikin matsala

Real Madrid ta kori Rafa Benitez daga aikinsa na horas da kungiyar, bayan watanni bakwai kacal da aka ba shi mukamin.

Real Madrid din ta nada Zinedine Zidane a matsayin kociyan rikon kwarya, sannan Santi Solari zai taimaka masa wajen gudanar da aikin.

Benitez ya jagoranci Madrid wasanni 25 tun lokacin da ya koma Bernabeu da horas da tamaula, inda ya ci wasanni 17 aka doke shi sau biyar sannan ya yi canjaras a karawa uku.

A kuma ranar uku watan Yunin bara, Real Madrid ta nada Benitez a matsayin kociyanta, bayan da ta sallami Carlo Anceloti.

Benitez din ya kasa lashe manyan wasannin hamayya da Madrid ta buga da Villareal da Sevilla da kuma Barcelona, kuma ta raba maki tsakaninta da Atletico Madrid da Valencia.