Ina son horas da tamaula a Ingila - Guardiola

Hakkin mallakar hoto allsport
Image caption Guardiola ya horas da Barcelona kafin ya koma Bayern Munich

Pep Gaurdiola ya ce ya amince ya bar Bayern Munich domin ya koma horas da kwallon kafa a Ingila.

Tun a can baya Guardiola ya ce ba zai tsawaita zamansa a Jamus ba, idan kwantiraginsa ya kare a bana.

Ana rade-radin cewa kociyan zai koma horas da tamaula ne a Manchester City ko Manchester United ko Chelsea ko kuma Arsenal.

Shugaban Bayern Munich, Karl-Heinz Rummenigge, ya ce tuni Gaurdiola ya san kungiyar da zai kama aiki da ita.

Sai dai kuma a wani taro da aka yi da shi da 'yan jarida kociyan ya ce har yanzu bai yanke shawarar kungiyar da zai koma horas da kwallon kafa ba.

Tuni Munich din ta dauki Carlo Ancelotti a matasyin wanda zai maye gurbin Guardiola, wanda ya ce kungiyar ta yi farar dabara.