Na yi alfaharin horas da Madrid - Benitez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Litinin ce Real Madrid ta raba gari da Rafael Benitez

Kwana daya da Real Madrid ta sallami Rafael Benitez daga koci ya ce martaba ce da kuma girmamawa da ya horas da kungiyar.

Madrid ta sallami Benitez ne bayan da mahukuntan kungiyar suka kammala taron da suka yi a ranar Litinin, inda suka maye gurbinsa da Zinedine Zidane.

Wasanni uku kawai aka doke Real Madrid a karawa 25 da ya jagoranci kungiyar, sannan ya kai ta wasan zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai.

A wani sako da Benitez din ya fitar ya ce yana mai goyon bayan nada Zidane da aka yi a matsayin kocin rikon kwarya sannan yana marawa 'yan wasan kungiyar baya.