CAF ta nada alkalan gasar kofin Afirka na 2016

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption Za a fara gasar cin kofin Afirka a Rwanda a ranar 16 ga Janairu zuwa 7 ga watan Fabrairu

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta nada alkalan da za su busa wasa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke taka leda a gida da za a yi a bana.

Caf din ta nada alkalai 34, kuma16 daga cikinsu ne za su jagoranci wasannin da za a yi, inda 18 su taimaka musu gudanar da aikin.

Kasar Rwanda ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da suke murza leda a gida da za a fara daga ranar 16 ga watan Janairu zuwa bakwai ga watan Fabrairu.

Ga jerin alkalan da za su busa gasar cin kofin Afirka:

 1. Abid Charef Medhi Algeria
 2. Bernard Camille Seychelles
 3. Denis Dembele Cote d'Ivoire
 4. Ibrahim Nour El Din Masar
 5. Daniel Bennet Afirka ta Kudu
 6. Kordi Med Said Tunisia
 7. Mohamed H. El Fadil Sudan
 8. Nampiandraza Hamada Madagascar
 9. Keita Mahamadou Mali
 10. Ali Lemghaifry Mauritania
 11. Malang Diedhiou Senegal
 12. Zio Ephrem Juste Burkina Faso
 13. Davies Omweno Kenya
 14. Hudu Munyemana Rwanda
 15. Joseph Lamptey Ghana
 16. Thierry Nkurunziza Burundi

Mataimakan alkalin wasa:

 1. Mokrane Gourari Algeria
 2. Ndagijimana Theogene Rwanda
 3. Mark Ssonko Uganda
 4. Oamogestse Godisamang Botswana
 5. Noupue Nouegoue Elvis Kamaru
 6. Dina Bienvenu Benin
 7. Serigne Cheikh Toure Senegal
 8. Ahmed Hossam Taha Masar
 9. Tesfagiorghis Berhe Eritrea
 10. David Laryea Ghana
 11. Mamady Tere Guinea
 12. Sullaymane Sosseh Gambia
 13. Marwa Range Kenya
 14. Mahamadou Yahaya Nijar
 15. Hensley Petrousse Seychelles
 16. Khumalo M. Steven Afirka ta Kudu
 17. Theophile Vinga Gabon
 18. Nabina Blaise Sebutu Jamhuriyar Congo