An tsawaita dakatarwar da aka yi wa Valcke

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Valcke da yin almubazzaranci da kuma karya dokokin FIFA.

Alkalai a hukumar kula da kwallon kafar duniya, FIFA, sun tsawaita dakatarwar da aka yi wa Sakatare Janar na hukumar, Jerome Valcke daga shiga harkokin wasanni da kwanaki 45.

Alkalan za su yi nazari kan shawarar da kwamitin da'a na hukumar ya bayar ranar Talata cewa ya kamata a dakatar da Mista Valcke daga harkokin wasanni tsawon shekara tara, sannan a ci shi tarar kimanin £100,000 a kan zargin karbar hanci.

Ana zarginsa da yin almubazzaranci da kuma karya dokokin FIFA.

Mista Valcke ya sha musanta zargin.