Juventus ta lashe wasanni takwas a jere

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Juventus tana mataki na uku a kan teburin Serie A

Juventus ta doke Verona da ci 3-0 a gasar Serie A, a wasan da suka buga na mako na 18 a ranar Laraba.

Paulo Dybala ne ya ci kwallon farko, Leonardo Bonucci ya ci ta biyu, sannan Simone Zaza ya kara ta uku.

Hakan kuma ya sa kungiyar wadda ta dauki kofin Serie A na bara, ta lashe wasannin gasar sau takwas a jere.

Da kuma wannan sakamakon tana mataki na uku a kan teburin gasar ta Italiya da maki 36.

A sakamakon sauran wasannin da aka yi, Inter Milan, wadda take mataki na daya a kan teburin, ta doke Empoli da ci daya mai ban haushi.

AC Milan kuwa rashin nasara ta yi a gida da ci daya babu ko daya a hannun Bologna, inda Lazio da Carpi suka tashi canjaras.

Ga sakamakon wasannin gasar Serie A da aka yi:

  • Juventus 3 - 0 Verona
  • Empoli 0 - 1 Inter Milan
  • Udinese 2 - 1 Atalanta
  • Chievo 3 - 3 Roma
  • Lazio 0 - 0 Carpi
  • Milan 0 - 1 Bologna
  • Palermo 1 - 3 Fiorentina
  • Sassuolo 2 - 2 Frosinone