An haramtawa jami'an IAAF shiga wasanni

Image caption Ana zargin jami'an IAAF da yin rufa-rufa a kan shan kwayoyin kara kuzari da 'yan wasan Rasha su ka yi.

An hana wasu jami'an hukumar guje-guje da tsalle-tsalle na duniya su uku daga shiga wasannin har tsawon rayuwarsu.

Ana zarginsu ne da yin rufa-rufa a kan shan kwayoyin kara kuzari da 'yan wasan Rasha su ka yi.

Kwamitin da'a na hukumar gudanarwa na IAAF, ya ce hukuncin da aka yanke musu ya yi dai dai da karfin laifin da suka aikata.

Mutanen da aka haramtawa sun hada da Papa Massata Diack -- dan tsohon shugaban hukumar ta IAAF, Lamine Diack, da kuma tsohon shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Rasha, Valentin Balakhnichev.

Ana dai zarginsu ne da karbar cin hanci domin rufe badakalar.