Debuchy zai bar Arsenal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aston Villa na zawarcin Debuchy

Arsene Wenger ya ce dan wasansa Mathieu Debuchy zai iya barin kungiyar a kasuwar musayar 'yan kwallo.

Aston Villa wacce ke matakin karshe a teburin gasar Premier, ta na zawarcin dan kwallon mai shekaru 30.

"Mathieu na da damar barinmu amma ba mu ji daga wata kungiya ba," in ji Wenger.

A yanzu haka dai Arsenal na ci gaba da tattaunawa da dan kwallon Masar, Mohamed Elneny wanda suka son saya daga FC Basel a kan fan miliyan biyar.

Arsenal na kokarin kara karfin tawagarta, saboda Francis Coquelin da Santi Cazorla da Aaron Ramsey da Mikel Arteta da kuma Jack Wilshere suna fama da jinya.