'Da wuya Nigeria ta lashe gwarzon dan kwallon Afirka'

Image caption Abba Yola tsohon ma'aikaci a hukumar wasanni ta Nigeria

Za a dauki lokaci mai tsayo kafin dan Nigeria ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka da ake karramawa a duk shekara in ji Abba Yola.

A ranar Alhamis ne hukumar kwallon kafa ta Afirka ta bayyana dan kwallon Gabon mai taka leda a Borussia Dortmund, Pierre-Emerick Aubameyang, a matsayin wanda ya lashe kyautar dan kwallon Afirka da ya fi yin fice a Abuja Nigeria.

Abba Yola tsohon ma'aikacin hukumar wasanni ta Nigeria ya ce yanzu Nigeria ba ta da fitattun 'yan wasan kwallon kafa wadanda ke taka leda a manyan gasar kasashen Turai.

Ya kuma kara da cewar kyautar ba ta tsaya kan bajintar da 'yan wasa ke yi a fagen murza leda ba, har da gudunmawar da dan kwallo ke bayarwa wajen ci gaban tamaula a Afirka.

Abba Yola tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Kano Pillars ya kuma ce sai 'yan kwallon Nigeria sun zage damtse kafin a samu wanda zai lashe kyautar a nan kusa.

Rabon da Nigeria ta lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka tun wadda Kanu Nwankwo ya lashe a shekarar 1999.

Rashidi Yekini da Emmanuel Amuneke da Daniel Amokachi da Victor Ikpeba da Sunday Oliseh da Jay-Jay Okocha da Kanu Nwankwo sune suka lashe kyautar a baya.