Chelsea ta doke Scunthorpe United 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 14 a kan teburin Premier

Chelsea ta kai wasan zagayen gaba a kofin FA bayan da ta doke Scunthorpe United da ci 2-0 a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Chelsea wadda ta buga wasan a Stamford Bridge ta ci kwallon farko ne ta hannun Diego Costa a minti na 13 da fara tamaula.

Mai tsaron ragar Scunthorpe, Luke Daniels ya hana kwallon da Cesc Fabregas da kuma Pedro suka buga masa shiga raga.

Chelsea ta zura kwallo ta biyu a raga ne bayan da Ruben Loftus ya ci gida a minti na 68.