Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2015

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na biyar Messi yana lashe kyautar Ballon d'Or

Dan wasan Argentina da Barcelona, Lionel Messi, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta duniya ta ballon d'Or ta 2015.

Kyaftin din na Argentina mai shekara 28, ya doke Cristiano Ronaldo ne na Portugal da Real Madrid da Neymar na Brazil da Barcelona.

Messi ya zura kwallaye 59 a raga cikin wasanni 66 da ya buga wa kasarsa da kungiyarsa, kuma karo na biyar da Messi ya samu kyautar kenan bayan da ya taba lashe ta a 2009 da 2010 da 2011 da 2012.

Messi ya dauki kofuna biyar a shekara ta 2015 da suka hada da na La Liga da na Copa del Rey da kofin zakarun Turai da UEFA Super Cup da kuma na zakarun nahiyoyin duniya.

Wannan ce shekara ta takwas a jere da Ronaldo, dan kwallon Real Madrid, da dan wasan Barcelona Messi ke shiga cikin 'yan takara.

Wannan shi ne karon farko da Neymar ya shiga cikin jerin 'yan takara uku na karshe a kyautar ta Ballon d'Or.