Klopp ya shawarci Guardiola kan gasar Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Klopp da Guardiola sun yi hammaya a Jamus

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya gargadi Pep Guardiola cewa akwai babban kalubale da zai fuskanta a gasar Premier ta Ingila saboda ana buga wasanni da dama.

Klopp ya shawarci Guardiola cewa yanayi a Biritaniya babu dadi sosai, amma kuma abinci a Ingila, ya fi "yadda mutane ke fadi".

Guardiola mai shekaru 44, zai bar Bayern Munich a karshen kakar wasa ta bana, kuma ya bayyana cewa yana shirin yin aiki a Ingila a kakar wasa mai zuwa.

Dan kasar Spain din ana tunanin zai je ko Manchester City, Chelsea ko kuma Manchester United.

Klopp ya ce "Ana buga wasanni da yawa, kuma shi ne bambamcin."