Real Betis ta sallami kociyanta Pepe Mel

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau biyu Pep Mel ya jagoranci Real Betis, ya kuma horas da West Brom

Real Betis ta raba gari da Pep Mel, bayan da ya kasa tabuka rawar gani a wasannin da ya jagoranci kungiyar a gasar La Ligar Spaniya.

Mel ya karbi aikin horas da Betis a karo na biyu a watan Disambar 2014, inda ya kai kungiyar matakin buga babbar gasar ta Spaniya.

Sai dai kuma Betis ta kasa tabuka rawar gani a bana, kuma doke ta 1-0 da Getafe ta yi a ranar Asabar ya sa kungiyar a mataki na 15 a kan teburin La Liga.

West Brom ta dauki Mel a matsayin kociyanta a watan Janairun 2014, amma ta sallame shi daga aikin watanni hudu kacal.

Mel ya fara horas da Betis tsakanin Yulin 2010 zuwa Disambar 2013, sannan West Brom ta dauke shi aiki a watan Janairun 2014.