Shin Messi ne ya fi kowa iya kwallo ne ?

Hakkin mallakar hoto epa

Lionel Messi na Barcelona da Argentina yana da lambar yabo guda biyar ta gwarzon dan kwallon kafar da ya fi yin fice a duniya da ya lashe. Babu kuma wani mahaluki da ya kusan kama kafarsa. Shin Messi ne ya fi koya iya kwallo da ba kamarsa kenan?

'Gaskiya ne'

Bisa nasarorin da Messi ya samu a kungiyarsa hakika babu kamarsa.

Kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ya lashe karo na biyar shaida ce da ta fayyace yadda dan wasan ke taka rawar gani a kowacce kakar wasa, kuma daya daga cikin fitaccen dan wasan Barcelona da ke saka mata rigar da yake wakiltarta.

Messi ya kasance fitacce a cikin 'yan wasan tamaula cikin shekara 10, kusan shekaru goma da suka wuce shi kadai ya dagulawa Chelsea lissafi a gasar cin kofin zakaru wasan kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Bai kuma tsaya a nan ba, ya ci gaba da nuna bajintarsa, wanda tsohon dan kwallon tawagar Argentina, Diego Maradona daya daga cikin mutane biyu da aka bai wa sarautar kwallon kafa ba zai iya taka rawar da ya yi ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

A shekara ta 2007 aka fara zabar Messi a cikin 'yan takara Ballon d'Or inda ya yi na uku a zaben, Cristiano Ronaldo lokacin yana wasa a Manchester United ya yi na biyu, Kaka na AC Milan ya yi na uku. Kuma tun daga shekarar ne daya daga cikin Messi ko Ronaldo suka dunga lashe kyautar.

Messi na kara bunkasa a wasan da yake yi daga shekara zuwa shekara, har yanzu bai cika shekara 30 da haihuwa ba, amma yadda yake cin kwallaye ya sa ya zama dan wasan Barcelona da ya fi ci mata kwallaye tun yana da shekara 25 da haihuwa.

Yanzu haka yana rike da tarihin dan wasan da ya fi cin kwallaye a gasar La Liga a kaka guda, inda ya zura 50, ya kuma ci kwallaye 91 a shekara daya, ya zura kwallaye biyar a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma shi ne ya fi kowa yawan zura kwallaye a gasar ta zakarun Turai inda ya ci biyar a raga.

Wannan ne ya nuna hazakar da yake da ita a tamaula, saboda hamayyar da ake yi tsakanin 'yan wasa a gasar ta cin kofin zakarun Turai ta yi nisa matuka.

Duk wanda ya karbi kyautar Ballon d'Or a hannun Messi sai kaga ba a shekarar da ake buga gasar cin kofin duniya ba ne, kuma dan wasan bai wuce su kara da manyan kungiyoyi biyu ba sannan su lashe kofin zakarun Turai.

A yanzu kuwa duk kungiyar da za ta lashe kofin zakatun Turai sai ta fuskanci barazana daga fitacciyar kungiya daga Ingila ko Jamus ko Italiya ko Spaniya ko Holland da sauransu a kowanne wasan da za ta buga a mako, kuma hakan bai hana Messi cin kwallaye akai-akai.

Kuma yana cin kwallayen ne cikin murmushi da annashuwa, daya daga cikin dalilan da ya sa mutane ke kaunarsa a duniya, ba kamar abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ba.

'Ba gaskiya ba ne'

A kullum muhawarar da ake yi kenan cewar, waye ya fi fice a fagen tamaula a duniya.

Babu tantama 'yan wasa biyu aka sani a baya da babu kamarsu a iya murza-leda da suka hada da Pele da kuma Maradona.

Hakkin mallakar hoto AFP

A gasiya dai Pele shi ne dan kwallon da ya lashe kofuna uku a gasar cin kofin duniya, duk da cewar kwallaye 1,281 da ya ci a wasanni 1,363 shi ne na uku a yawan zura kwallaye a raga a tarihi, amma kuma shaidace da ke nuna cewar fitaccen dan wasan kwallon kafa ne da ya yi suna a duniya, kuma kwakkwarar hujja ce..... sai dai ba ta kai kalubantar da Messi ke fuskanta a kowanne mako ba.

Hakkin mallakar hoto AP

Koda yake Maradona kofin duniya guda daya ya lashe a shekarar 1986, kuma ana mai kallo shi kadai ya jagoranci kasarsa ta Argentina lashe kofin a lokacin.

Kwallo ta biyu da ya ci Ingila a wasan daf da na kusa da karshe a gasar ta kofin duniya, ya ci kwallo ta ban sha'awa a cikin dakika 10.

Ya kuma taba yin haka a kungiyarsa ta Napoli, inda ya jagorance ta lashe kofin kasar Italiya a shekarar 1987 da kuma 1990 da kuma kofin Uefa a 1989.

A bangaren Messi kuwa ya dara tsara duk da yana murza-leda ne a kungiyarsa tare da zakakuren 'yan wasa da suka hada da Iniesta da Xavi da Luis Suarez da kuma Neymar.

Lokacin da Messi ya ji rauni kuma zai yi jinyar watanni biyu, nan da nan Barcelona ta umarci Neymar da ya kara kwazo, kuma hakan aka yi inda kungiyar ta ci gaba da lashe wasannin da ta dunga yi.

Argentina na dogara ne a kan Messi ya haskaka a gasar cin kofin duniya da ta Copa America, kuma hakan ne ke faruwa.

Kwallayen da ya ci a gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 2014 sun taimakawa Argentina kaiwa wasan karshe, sai dai kuma a karawar karshen da suka yi da Jamus bai taka rawar gani ba, har aka cire su a bugun fenariti.

Sai dai kuma a lokacin Pele da Maradona babu wanda ya samu damar shiga takarar Ballon d'Or saboda a lokacin ana karrama dan wasan da ya fi yin fice a tamaula a nahiyar Turai -- saboda haka ba za a kwanta su da lashe kyautar ba.