Newcastle da Man United sun tashi 3-3

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Newcastle United da Manchester United sun buga 3-3

Newcastle United da Manchester United sun buga 3-3 a gasar Premier wasan mako na 21 da suka yi a St James Park ranar Talata.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Rooney a minti na tara da fara wasa, sannan Lingard ya kara ta biyu a minti na 38.

Daf da za a tafi hutu ne Wijnaldum ya ci wa Newcastle kwallo, sannan Mitrovic shi ma na Newcastle ya ci ta biyu a bugun fenariti.

United ta ci kwallo ta uku ne ta hannun Rooney kuma Newcastle ta farke kwallon ta hannun Dummett daf da za a tashi daga fafatawar.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Aston Villa ta ci Crystal Palace daya da babu ko daya a Villa Park, yayin da West Ham United ta doke Bournemouth 3-1 har gida.