An fitar da jadawalin gasar Firimiyar Nigeria

Image caption Shehu Dikko shugaban hukumar gudanar da gasar Firimiyar Nigeria

Hukumar da ke kula da gasar cin kofin Firimiyar Nigeria ta fitar da jadalin wasannin da za ta gudanar a kakar wasan 2015 zuwa 2016.

Hukumar ta tsara cewar za a fara buga gasar Super 4 sau biyu a bana, wasan farko a Kaduna daga 20 ga watan Janairu zuwa 24 ga watan.

Karawa ta biyu kuwa za a yi ne a Akwa Ibom daga daya ga watan Fabrairu zuwa biyar ga watan.

Haka kuma hukumar ta tsayar da ranar 21 ga watan Fabrairu domin fara gasar Firimiya bana a kuma kammalata ranar biyu ga watan Oktoban 2016.

Hukumar ta kuma umarci kungiyoyin da ke buga gasar da su biya dukkan hakkin 'yan wasa da suke bin su na kakar wasan 2014/15 kafin nan da 10 ga watan Fabrairu.

Ta kuma tsaida ranar 15 ga watan Fabrairu mai zuwa domin kungiyoyin su kammala yin rijistar 'yan wasa da za su fafata a gasar ta bana har da yi musu inshora.