Shelvey ya koma Newcastle United

Image caption Shelvey shi ne dan wasa na biyu da ya koma Newcastle

Newcastle United ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Swansea City dan Ingila Jonjo Shelvey a kan kudi fan miliyan 12.

Sai da likitocin Newcastle United suka duba lafiyar dan kwallon mai shekaru 23, sannan ya kulla yarjejeniyar taka leda a St James Park.

Shelvey ne dan kwallo na biyu da zai koma Newcastle a cikin watan Janairu, bayan dan Senegal Henri Saivet wanda ya koma St James Park daga Bordeaux.

A shekara ta 2013, Shelvey ya koma Swansea daga Liverpool a kan fan miliyan biyar, kuma a shekara 2015 ne ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da buga wa Swansea City tamaula shekara hudu da rabi.

Shelvey ya buga wa Ingila wasanni sau shida.