FIFA ta kori Jerome Valcke

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An kori Valcke ne bayan an same shi da laifin karbar hanci.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta kori Sakatare Janar dinta, Jeroma Valcke.

Ana zargin sa ne da hannu a karbar hancin dala miliyan 10.

An yi zargin cewa an bai wa Jack Warner, tsohon shugaban hukumar kwallon kafar arewaci da tsakiyar Amurka, hancin ne domin shi kuma ya goyi bayan Afrika ta kudu ta karbi bakwancin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010.

Valcke ya sha musanta zargin.

A watan Oktoban da ya gabata aka dakatar da shi daga shiga duk harkokin kwallon kafa.