Roma ta kori kociyanta Rudi Garcia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rudi Garcia ya horas da kungiyar Lille ta Faransa

Roma ta sallami Rudi Garcia daga aikin horas da kungiyar, bayan da ya kasa tabuka rawar gani a gasar cin kofin Serie A ta Italiya.

Garcia tsohon wanda ya koyar da Lille tamaula ya lashe wasa daya da ya ci Genoa 2-0 tun farkon watan Nuwambar 2015.

Roma za ta fafata da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai wasan kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

An nada Alberto de Rossi mahaifin mataimakin kyaftin Daniele domin ya jagoranci kungiyar wasanninta na gaba.