An hana Madrid da Atletico sayen 'yan wasa

Image caption Atletico ce ke mataki na daya a kan teburin La Liga, Madrid tana matsayi na uku a teburin

An dakatar da Real Madrid da Atletico Madrid daga sayo sabbin 'yan wasan kwallon kafa tsawon shekara biyu.

Hukumar kwallon kafar duniya Fifa ce ta dakatar da kungiyoyin biyu bisa samunsu da tayi da laifin karya ka'idar daukar matasan 'yan wasan tamaula.

Dakatarwar da aka yi musu za ta fara aiki ne bayan kammala cinikin kasuwar Janairun nan da ke ci a yanzu.

Haka kuma Fifa ta ci tarar Atletico 900,000 kudin Swiss Frans, yayin da Real Madrid za ta biya 360,000.

Fifa ta taba dakatar da Barcelona daga sayen 'yan wasan kwallon kafa a watan Afirilun 2014 kan karya ka'idar sayen 'yan wasa matasa 'yan kasa da shekara 18.

A kuma watannan ne wa'adin da aka yanke wa Barcelona ya cika.