Ighalo ne gwarzon watan Disamba a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ighalo da kocinsa sun haskaka

Dan Najeriya wanda ke murza leda a Watford, Odion Ighalo ya ce ya ji dadain samun kyautar gwarzon dan wasan Premier na watan Disamba.

"Na zura kwallaye, amma wannan nasarar ba tawa bace ki kadai," in ji Ighalo.

Ighalo mai shekaru 26, ta zura kwallaye biyar a cikin watan Disamba, kenan ya ci kwallaye 13 a kakar wasa ta bana.

Shi ma kocin Watford, Quique Sanchez Flores an ba shi kyautar koci mafi bajinta a watan Disamba.

Wannan ne karon farko da dan wasan Watford ya samu kyautar.