Spalletti zai ja ragamar Roma karo na biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Roma za ta fafata da Real Madrid a gasar cin kofin Zakarun Turai

Roma ta nada Luciano Spalletti, a matsayin sabon kociyanta kuma karo na biyu kenan da zai jagoranci kungiyar.

Spalleti mai shekara 56, zai maye gurbin Rudi Garcia wanda Roma ta sallama daga aiki a ranar Laraba.

Ya fara horas da Roma tun daga 2005 zuwa 2009, inda ya lashe kofunan Coppa Italiya biyu, daga nan kuma ya koma Zenit St Petersburg ta Rasha.

Spaletti dan kasar Italiya ya lashe kofin gasar Rasha daya amma kuma Zenith ta kore shi daga aiki a shekarar 2014.

Roma za ta kara da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.