Manchester City ta dauko Caceres

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Caceres ya haskaka a Australia

Kungiyar Manchester City ta siyo Anthony Caceres daga kungiyar Central Coast Mariners ta kasar Australia.

Dan shekaru 23, Caceres ya koma Mariners ne a shekarar 2012, inda ya zura kwallaye uku a wasanni 62.

Kocin Mariners Tony Walmsley ya ce "Akwai dadi idan aka sayar da dan wasa zuwa babbar kungiyar."

Dan kwallon na kasar Australia shi ne na farko da City ta siyo a watan Janairu.