Copa del Rey: Barca za ta kara da Athletic Bilbao

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barcelona tana matsayi na biyu a kan teburin La Liga

Barcelona za ta kara da Athletic Bilbao a gasar Copa del Rey wasan daf da na kusa da karshe.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar a bara a wasan karshe, inda Barcelona ta doke Athletico Bilbao da ci 3-1.

Valencia wadda Garry Neville ke jagoranta za ta fafata ne da Las Palmers, Celta Vigo kuwa ta barje gumi da Atletico de Madrid.

Sevilla kuwa za ta fafata ne da CD Mirandes.

Za su fara karawa a ranar 20 da kuma 21 ga watan Janairun a wasan farko, wasa na biyu kuwa za su yi ne a ranar 27 ga watan.