Autan Faya ya buge Shagon Bahagon Musa

Image caption Autan Faya daga Kudu da Shagon Bahagon Musa daga Arewa

A wasan damben gargajiya da aka dambata a ranar Asabar da yammaci a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria an dambata a wasanni biyar.

Wasan farko tashi aka yi babu kisa tsakanin Bahagon Soja daga Arewa da Shagon Shagon Autan Sikido daga Kudu kuma turmi uku suka yi.

Nan da nan aka sa zare tsakanin Shagon Jafaru daga Kudu da Shagon Buzu daga Arewa, Turmi uku suka fafata amma babu kisa a wasan.

Daga nan ne kuma aka yi wasan da Autan Faya daga Kudu ya kashe Shagon Bahagon Musa daga Arewa a turmi na biyu.

Karawa tsakanin Bahagon Dakaki daga Kudu da Bahagon Musan Kaduna daga Arewa ta kayatar, sai dai turmi biyu suka yi babu kisa aka raba su.

Wasan karshe kuwa an yi shi ne tsakanin Shagon Inda daga Arewa da Abbati daga Kudu, kuma turmi biyu suka taka, aka raba su saboda dare ya yi, watakila su kara karawa a ranar Lahadi da safe.