Manchester ya dare saman tebur

Image caption Sergio Aguero

Kulob din Manchester City ya samu nasarar dare wa kololuwar teburin Premier, bayan da ya lallasa kungiyar wasa ta Crystal Palace da ci 4 da nema.

Kulob din na Manchester dai ya fara wasan ne kamar za a yi kamar ba za a yi ba, amma daga bisani sai dan wasan tsakiyar kungiyar, Fabian Delph ya daga ragar Crystal Palace da kwallon farko.

Sergio Aguero ya kara ta biyu da a uku a ragar ta Crystal Palace.

Shi kuma David Silva ya zarga kwallo ta hudu, abin da ya ba wa kulob din nasa dabar dare wa bisa teburin Premier.