Likitoci na duba lafiyar Diego Costa

Hakkin mallakar hoto Rex Feature
Image caption Chelsea tana mataki na 14 a kan teburin Premier

An kai dan wasan Chelsea, Diego Costa asibiti domin su duba girman raunin da ya ji a karawar da suka tashi 3-3 a gasar Premier da Eveton a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekara 27, ya ci kwallaye biyu a karawar, kuma saura minti 10 a tashi daga wasan ne ya fadi a cikin fili inda aka dauki lokaci mai tsawo ana duba lafiyarsa.

Costa ya ci kwallaye biyar a wasanni biyar da ya buga tun lokacin da Guus Hiddink ya maye gurbin Jose Mourinho a Stamford Bridge.

Dan wasan shi ne wanda ya fi ci wa Chelsea kwallaye a gasar Premier bara, inda ya zura 20 a raga.