Ranieri na harin maki 79 a karshen gasar Premier

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Leicester tana da maki 44 daga wasanni 23 da ta buga a gasar Premier

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri, ya bukaci 'yan wasansa da su kare zage damtse su kuma kammala gasar Premier bana da maki 79.

Leicester wadda ta buga 1-1 da Aston Villa a ranar Asabar, tana da maki 44 daga wasanni 23 da ta buga a gasar.

Kociyan ya ce sun kammala buga wasannin zagayen farko da maki 39, saboda haka ne ya bugaci 'yan wasa da su saka kaimi su sami maki 40 a wasannin zagaye na biyu da suke yi.

Ya kuma kara da cewar hakan kalubale ne mai wahala, amma hakan ne zai sa su lashe kofin bana ko kuma su samu gurbin buga gasar cin kofin zakarun Turai a badi.

Sau uku ne aka samu kungiyoyin da suka lashe kofin Premier da maki 79 ko kuma kasa da hakan, amma sauran kofunan an lashe su ne da maki masu yawa.