Man United ta samu maki uku a Anfield

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta kai mataki na biyar a kan teburin Premier

Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 1-0 a gasar Premier wasan mako na 22 da suka kara a Anfield a ranar Lahadi.

Wayne Rooney ne ya ci wa United kwallo saura minti 11 a tashi daga wasan, wanda rabon da ya ci kwallo a Anfield tun a shekarar 2005.

Kwallon da Rooney ya ci ita ce ta 176, hakan ya sa ya kafa tarihin dan wasan da ya fi yawan cin kwallaye a kungiya daya a Ingila, Terry Henry wanda ya yi Arsenal yana da kwallaye 175.

Rooney ya ci kwallaye hudu a jere a wasannin gasar ta Premier da ya yi, yana da guda shida jumulla da ya ci kenan a bana.

Da wannan nasarar United ta koma mataki na biyar a kan teburi da maki 37, ita kuwa Liverpool tana da maki 31 a matsayi na tara a kan teburin.