Zidane ya jagoranci Madrid lashe wasa na biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ta hada maki 43 daga wasanni 20 da ta yi a La Liga

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya jagoranci kungiyar lashe wasa na biyu, inda suka doke Sporting Gijon a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Real Madrid din ta doke Sporting Gijon ne da ci 5-1 a karawar da suka yi a filin wasa na Bernabeu wasan gasar mako na 20.

Minti 18 da fara wasan ne Madrid ta ci kwallaye hudu ta hannun Bale da Ronaldo wanda ya ci biyu da kuma Benzema, wanda ya kara ta biyar saura minti hudu a je hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma Bale da Benzema sun ji rauni a fafatawar, inda Jese ya canji Bale, Kovacic ya maye gurbin Benzema.

Sporting Gijon ta zare kwallo daya ne ta hannun Isma Lopez, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Tuni dai hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta dakatar da Real Madrid da Atletico Madrid daga sayo sabbin 'yan wasan kwallon kafa tsawon shekara biyu.

Fifa ta ce ta dakatar da kungiyoyin biyu bisa samunsu da tayi da laifin karya ka'idar daukar matasan 'yan wasan tamaula.