Man Utd zai iya daukar kofin Premier — Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Van Gaal ya ce suna da kwarin gwiwar daukar kofi.

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce kulob din yana sa ran daukar kofin Premier na Ingila na bana.

Van Gaal ya bayyana haka ne bayan sun doke Liverpool da ci 1-0 ranar Lahadi, lamarin da ya sa suka koma mataki na biyar a saman teburin gasar, watau tsiransu da Arsenal da ke saman teburin maki bakwai ne kawai.

Da aka tambaye shi ko yaya yake ganin damar kulob dinsa na daukar kofin, sai Van Gaal ya ce, "Har yanzu akwai kalubale a gabanmu. Za mu ci gaba da yin kokari, domin ba abu ne mai sauki ba. Amma za mu iya daukar kofin tunda duk mako muna nuna yiwuwar hakan."

Ya kara da cewa za su iya cike gibin da ke tsakaninsu da Arsenal da Leicester, wacce ke mataki na biyu a saman teburin gasar.