Al Ahly ta kori kociyanta Jose Peseiro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Oktoba Al Ahly ta dauki Jose Peseiro a matsayin kociyanta

Al Ahly ta raba gari da mai horas da 'yan wasanta Jose Peseiro, dan kasar Portugal.

Al Ahly ta sanar da korar kociyan mai shekara 55, a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

Kungiyar ta ce ta sallami Peseiro ne saboda ya kasa jure matsin da ya shiga da kuma kasa jure sukar da ake yi masa.

Al Ahly ta nada Abdel-Aziz Abdel-Shafi, a matsayin kociyan rikon kwarya, kuma karo na biyu kenan da yake jan ragamar kungiyar.