Ronaldo ya fi Messi cin kwallaye a bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana

Dan kwallon Portugal da Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya fi Lionel Messi na Barcelona yawan cin kwallaye a kakar wasan 2015/16.

Ronaldo, mai shekara 30, ya buga wasanni 28, ya kuma ci kwallaye 27 a bana, inda ya fara da cin kwallaye biyar a fafatawar da Madrid ta doke Espanyol 6-0 a ranar 12 ga watan Satumbar 2015.

Shi kuwa Messi, dan kwallon Argentina mai shekara 28, ya buga wasanni 23, inda ya ci kwallaye 19, ya kuma fara cin kwallaye biyu ne a kakar bana a karawar da Barcelona ta ci Sevilla 5-4 a Uefa Super Cup ranar 11 ga watan Agustan 2015.

Messi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana kuma karo na biyar, inda Ronaldo wanda ya lashe kyautar sau uku ya yi na biyu, Neymar ya yi na uku.