Gareth Bale zai yi jinyar makonni uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku kenan Gareth Bale yana jin rauni a bana

Dan kwallon Real Madrid, Gareth Bale zai yi jinyar makonni uku, kuma karo na uku kenan da yake jin rauni a bana.

Bale mai shekara 26, ya ji rauni ne a karawar da Madrid ta doke Sporting Gijon da ci 5-1 a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Wasu rahotanni daga Spaniya na cewa dan wasan na tawagar Wales zai yi jinyar makonni uku kafin ya dawo murza leda.

Ana kuma sa ran zai dawo buga wa Madrid tamaula a fafatawar da za ta yi da Roma a gasar cin kofin zakarun Turai.