Mignolet ya sabunta kwantaraginsa a Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ya yi wasanni goma sha biyar ba tare da an zura masa kwallo ko da guda daya a raga ba.

Mai tsaron ragar Liverpool Simon Mignolet ya sanya hannu a sabon kwantaragin shekara biyar a kulob din wanda zai kare a kakar wasa ta shekarar 2020-21.

Mignolet, mai shekara 27, ya koma Liverpool ne daga Sunderland a shekarar 2013 a kan fam miliyan tara, kuma ya yi wasa sau 122.

Dan wasan ya shaida wa shafin intanet na kulob din cewa, "Ni mutum ne da ke son shugabanci, da kuma ke son yin magana da sauran 'yan wasa a dakinmu na sanya tufafin kwallo da kuma bai wa 'yan wasan baya shawarwari kan yadda za su tsara wasansu".

Bajintar da ya yi ta wasanni goma sha biyar da ya buga ba tare da an zura masa kwallo ko da guda daya a raga ba, ta zarta ta duk wani mai tsaron raga a gasar Premier ta shekarar 2015.

An yi ta sukarsa bayan ya yi wani babban kuskure, musamman a wasan da suka tashi 3-3 da Arsenal, ko da ya ke kociyan kulob din Jurgen Klopp, ya mara masa baya.