West Ham ta dauki Sam Byram

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham United tana mataki na shida a kan teburin Premier

West Ham United ta dauki Sam Byram daga kungiyar kwallon kafa ta Leeds United.

Dan wasan mai shekara 22, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu da rabi, kuma Everton ma ta yi zawarcinsa.

Byram ya fara buga kwallo a makarantar horon matasa ta Leeds United tun yana da shekara 11, ya kuma fara buga wa babbar kungiyar wasa a watan Agustan 2012.

West Ham tana mataki na shida a kan teburin Premier da maki 36.