Ba zan bar Manchester City ba - Bony

Hakkin mallakar hoto Huw Evans Picture Agency
Image caption Kwallaye takwas Bony ya ci wa City a kakar wasannin bana

Dan kwallon Manchester City, Wilfred Bony, ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake yi cewar zai bar kungiyar.

Dan wasan ya tambayi Pellegrini dalilan da ya sa ba ya saka shi a wasanni a cikin watan Disamba, dalilin da ya sa ake cewar zai bar Ettihad a Janairun nan.

Bony ya koma Manchester City ne daga Swansea kan kudi fam miliyan 28, kan kwantiragin shekara hudu da rabi a shekarar 2015.

Dan wasan ya ci kwallaye takwas daga wasanni 23 da ya buga wa City a bana, amma aka daina sa shi a wasa tun lokacin da Sergio Aguero ya warke daga raunin da ya ji.

Bony ya ce yana jin dadin taka leda a City kuma ga shi suna buga gasar cin kofin zakarun Turai, kuma suna yin kokari a gasar Premier.