Liverpool na neman Teixeira

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alex Teixeira

Kulob din Liverpool yana son sayen dan wasan gaba na kungiyar wasan Shakhtar, Alex Teixeira, mai shekara 26 a kan kudi Fan miliyan 24 da rabi.

Ita ma kungiyar wasan Chelsea ana hasashen cewa tana son sayen dan wasan akan kudi kusan Fan miliyan 39.

Shi dai Teixeira ya zura kwallaye har 22, a wasannin League 15, sannan yana da kwallaye 4 a wasanni 10 na gasar kofin zakaran turai, Champions League ta bana.

Teixeira ya fara harkar kwallon kafa ne daga kulob din Vasco da Gama da ke Brazil kafin daga baya ya koma Shakhtar a 2010.

Liverpool dai ta zura kwallaye 25 ne kacal a wasanni 22 da ta buga na Premier League a wannan kakar.