Ashley Young zai yi doguwar jinya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ashley Young ya ji rauni a matsa-matsinsa.

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce dan wasan kulob din Ashley Young zai yi jinya mai tsawo saboda raunin da ya yi a matse-matsinsa.

A ranar Lahadi ne Young, mai shekara 30, ya ji raunin a wasan da suka doke Liverpool da ci daya da nema a Anfield.

Young, wanda ya koma United daga Aston Villa a shekarar 2011 a kan kwantaragin shekara biyar, ya buga wasa sau 23 a kakar wasa ta bana.

Nan gaba ne za a yi wa dan wasan tiyata.

Dan wasan yana daya daga cikin 'yan wasan da suke haskaka a United.