Valdes zai koma Standard Liege

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victor Valdes

Golan kulob din Manchester United, Victor Valdes ya yarda da ya koma kungiyar Standard Liege ta kasar Belgium, aro har zuwa karshen kakar wasannin Premier.

Valdes dai ya rattaba hannu kan kwantaragin zamansa a Man Utd har na watanni 18.

Sai dai kuma Victor Valdes din, mai shekara 34 wanda kuma tsohon Barcelona ne ya buga wa kulob din Manchester United din wasa biyu ne kacal, sakamakon rashin jituwarsa da van Gaal.

Ana sa ran cewa Valdes din zai koma Standard Liege din a watan January.