Chelsea ya doke Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diego Costa ne ya zura kwallo daya mai ban haushi.

Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta baras da damarta ta hawa saman teburin Premier bayan Chelsea ta zura mata kwallo guda mai ban haushi.

Arsenal, wacce ta buga wasan da 'yna kwallo goma, ta sha kashi ne a hannun Chelsea, wadda dan wasanta, Diego Costa, ya zura musu kwallo daya a filin wasa na Emirates.

Costa ya zura kwallon ne a didai lokacin da Arsnenal ke ci gaba da jin haushin jan katin da aka bai wa dan wasanta Per Mertesacker a minti na 18 da fara wasa saboda turewar da ya yi wa Costa a lokacin da ya ga yana kokarin jefa musu kwallo.

Minti biyar bayan Costa ya wartsake daga turewar da aka yi masa ne ya zura kwallon da Branislav Ivanovic ya tura masa.