Leicester na zawarcin Ahmed Musa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Musa

Kungiyar Leicester City wadda ke saman teburin Premier tana zawarcin dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa duk da cewa kungiyarsa CSKA Moscow ta ki yarda da farashin farko da kungiyar ta Ingila ta taya shi.

Kungiyar wasan ta Rasha dai ta ki yarda da Fan miliyan 15.1 da Leicester ta ce za ta biya a kan dan wasan, tana mai cewa Fan miliyan 18.9 take bukata.

An ba wa Leicester zuwa ranar daya ga watan Fabrairu lokacin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa, da taa kara kudi a kan dan wasan.

Musa dai wanda tsohon dan wasan VVV Venlo ne, ya ci kwallaye 10 a wasanni 29 a wannan kakar wasannin sannan kuma ya ci wa Najeriya kwallaye 11 a wasanni 56.