Tennis: Serena ta lallasa Sharapova

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Serena Williams

A karo na 18 a jere , Serena Williams tana samun damar zuwa wasan kusa-da-na-karshe a gasar Australian Open bayan da ta lallasa Maria Sharapova.

Serena wanda ita ce mai rike da kambun wasan kuma 'yar wasa mai matsayi na daya ta lallasa Sharapova mai matsayi na biyar da ci 6 da 4 da 6 da 1 a Melbourne Park.

'yar wasan dai na neman daukar kofi a gasar ta Australian Open karo na 22, za ta fafata da 'yar wasa mai matsayi na hudu Agnieszka Radwanska.

A wasan maza kuma, Roger Federer zai hadu da Novak Djokovic a wasan kusa-da-na-karshe