Crystal Palace ta karbi aron Adebayor

Hakkin mallakar hoto Crystal Palace
Image caption Adebayor zai ci gaba da murza leda a Crystal Palace

Kungiyar Crystal Palace ta karbi aron Emmanuel Adebayor zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Tun daga watan Satumba Adebayor, mai shekarar 31, ke zaune babu kulob, bayan da kungiyar Tottenham ta sake shi.

Dan wasan ya zurawa Totenham da Arsenal da kuma Manchester City kwallaye 94 a gasar Premier.

A makonnin da suka wuce ne kocin Palace, Alan Pardew, ya tabbatar cewa yana son sayen dan wasan dan kasar Togo.

Adebayor ya buga wasansa na karshe a Palace ne ranar uku ga watana Mayu na shekarar 2015, inda ya buga wasan minti shida, wanda Man City ta doke su da ci 1-0 a gidansu.