Murray, Konta sun kai zagayen kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Konta ta fice daga gasar Australian Open a bara ne tun a wasan cancanta

Shararren dan wasan Tennis Andy Murray da kuma Johanna Konta sun kai ga zagayen kusa da na karshe a gasar Australian Open.

'Yan wasan biyu dai dukkaninsu 'yan Biritaniya ne kuma wannan ne karo na farko da 'yan kasar biyu suka kai ga wannan mataki a Australian Open tun bayan shekarar 1977.

Konta ta ci gaba da haskakawa a gasar ne da ci 6-4 da 6-1, inda ta doke abokiyar karawarta 'yar China Zhang Shuai a zayen daf da na kusa da na karshe.

A dai gasar da ake yi a Melbourne, Andy Murray ya doke David Ferrer na Spaniya da ci 6-3 da 6-7(5-7) da 6-2 da kuma 6-3.

Konta ta ce "Burina tun ina karama shi ne na ga na lashe gasar Tennis."